Sabon Shugaban Jam’iyyar APC na Rikon Kwarya ya Dauki Matakin Farko

 

Gwamna Abubakar Sani Bello ya sanar da zaman majalisar NEC bayan zama shugaban riko na APC.

Gwamnan na jihar Neja ya hadu da ‘yan kwamitin CECPC, zai rage yawan ‘yan kwamitin zabe na kasa.

Zuwa gobe ne ake sauraron dawowar Mai Mala Buni daga kasar waje yayin da aka yi waje da shi.

Abuja – A wani yunkuri na tabbatar da zamansa shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya, Abubakar Sani Bello, ya kira taron majalisar koli na NEC.

Jaridar This Day ta ce sabon shugaban kwamitin na CECPC, Gwamna Abubakar Sani Bello ya yi zama na farko da sauran ‘yan majalisarsa na rikon kwarya.

A wajen wannan zaman a majalisar koli watau NEC za a tabbatar da zaman Abubakar Sani Bello shugaban APC. Wannan rahoto ya zo a gidan talabijin Arise.

Wata majiya ta ce sanarwar za ta ba jam’iyyar damar yin taron NEC nan da kwanaki bakwai.

Babban makasudin wannan zama shi ne yadda za a bullowa zaben shugabanni na kasa. Babu tabbacin cewa za a bijiro da maganar sauke Buni a wajen taron.

Zaftare yawan kwamitoci

Baya ga haka, Abubakar Sani Bello zai yi kokarin rage yawan kananan kwamitocin da Mala Buni ya kafa domin shirya zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa.

Rahoton ya ce wannan mataki da gwamnan jihar Neja zai dauka zai bada dama a tafi da sauran manyan jam’iyya, gwamnoni da ‘yan majalisa a aikin kwamitocin.

A karkashin jagorancin Buni, an nada mutane kusan 1700 a cikin kwamitocin da za su shirya zabe na kasa. Gwamna Bello yana ganin mutane 200 sun wadatar.

Sabon shugaban rikon kwaryan yana da ra’ayin cewa akwai bukatar duka kusoshin jam’iyya su sa baki wajen nada kwamitocin, ba a bar aikin ga mutum daya ba.

Mala Buni zai dawo gobe

A daidai wannan lokaci ne kuma ake samun labari cewa zuwa gobe ne ake sa ran dawowar gwamna Mai Mala Buni wanda aka sauke daga shugabancin CECPC.

Alamu na nuna cewa idan tsohon shugaban rikon kwaryan ya dawo Najeriya daga birnin Dubai, zai yi biyayya ga matakin da shugabannin APC suka dauka a jiya.

Buni ne shugaban APC – Akpanudoedehe

A jiya aka ji cewa jam’iyyar APC ta musanya sauyin shugaba, ta ce har yanzu Mai Mala Buni ne yake rike da CECPC, ta ce mutane su yi watsi da labaran da ke yawo.

Sanarwar ta fito ne daga bakin sakataren rikon kwarya, Sanata John James Akpanudoedehe. Ba a dade ba sai aka ga Abubakar Sani Bello a kan kujerar Mai Mala Buni.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here