Tinubu ya Kira Matar Mataimakin Shugaban Kasa a Matsayin Matar Shugaban Kasa
Bola Tinubu, shugaban jam’iyyar APC ya kara kwafsawa cikin furucinsa a karo na biyu.
Tinubu ya kira uwar gidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo da “matar shugaban kasa”.
Ya daki kwanon ne yayin da yake jawabi a ranar Alhamis yayin bikin kaddamar da tarihin Aisha Buhari Bola Tinubu, shugaban jam’iyyar APC, ya daki kwano a karo na biyu yayin gabatar da jawabi, The cable ta ruwaito.
Tsohon gwamnan jahar Legas din ya kira Dolapo Osinbajo, matar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da “matar shugaban kasa”.
Ya yi wannan kwafsawar ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da yake jawabi wurin kaddamar da ‘Tarihin Aisha Buhari: Mace ta musamman’.
Read Also:
An yi taron ne a dakin taro na Banquet Hall dake fadar shugaban kasa a Abuja.
Yayin da Tinubu yake wa jama’a jawabi ya ce:
“Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Mai girma matar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari; matar shugaban kasa, Dolapo Osinbajo.”
Bayan ya daki kwanon, sai da Tinubu ya dan dakata na ‘yan dakiku kafin ya cigaba da jawabinsa.
Dama Tinubu ya taba kwatankwacin hakan a ranar 29 ga watan Maris, inda yace a tura matasa miliyan 50 soja don su yi gyara akan lamarin tsaro.
Ya yi wannan furucin ne a Kano lokacin da yake shagalin cikarsa shekaru 69 da haihuwa.
Bayan yaduwar wannan jawabin nasa, ya yi gaggawar gyara akan kalamansa inda yace yana nufin matasa dubu 50 ba miliyan 50 ba.