Olusegun Obansanjo ya Kalubalanci Matasan Najeriya da Su Kawo Canji a Najeriya

 

Olusegun Obasanjo ya yi magana a kan matasa da harkar shugabancin Najeriya.

Tsohon shugaban ya ce matasan da ke tasowa ba za su tsinci mulki da araha ba.

Obasanjo ya ba matasa hakuri, ya yi kira gare su da su tashi su nemi shugabanci Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya kalubalanci matasan Najeriya da su kawo canji a Najeriya ta hanyar canza wanda zai rike shugabanci.

Da yake jawabi a wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa sa’o’insa sun aikata ba daidai ba iri-iri a Najeriya.

Kamar yadda jaridar Punch ta fitar da rahoto, an yi hira da tsohon shugaban kasar ne ta kafar yanar gizo, inda har ya ba matasa hakurin ta’asar da aka yi.

Olusegun Obasanjo ya yi kira ga matasan kasar da su yi abin da za su iya domin su hana dattawan da ya kira ‘tsofaffin kwanoni’ sakat a kujerun mulki.

Dattijon ya fada wa matasan cewa ka da su tsaya su na koka wa, domin su ne shugabannin gobe.

Obasanjo wanda ya yi mulkin farar hula tsakanin 1999 da 2007 ya ce tsofaffin da ke rike da madafan iko, ba za su bada mulki ta dadi ba, sai ‘an fatattake su.’

Ya ce: “Ku daina zama haka nan ku na kokawa. Zama ku na kuka ba zai kai ku ko ina ba, dole ku samu hadin-kan tulin mutane irinku da za su kawo sauyi.”

Obasanjo ya kara da cewa: “Idan mutane su ka ce yaushe tsofaffin nan za su tafi? Ina fada masu cewa ba za su tafi ba, sai dai ku yi abin da zai sa su bada wuri.”

“Haka nan ba za su bada mulki da kansu ba, sai dai idan kun hana su sake wa.” Inji Obasanjo.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here