Matashi ya Rasa Ransa Sanadiyyar Faɗawa Kwata a Kano

An gano wani matashi dan shekara 25, Ghaddafi Saleh, da ya faɗa Kwata a kan hanyar Zariya, yankin Tarauni a jihar Kano.

Jami’an hukumar kwana-kwana sun yi gaggawar kai masa ɗauki, suka tsamo shi cikin mawuyacin hali, daga baya ya cika

A ranar Lahadi da ta gabata, an yi wani mamakon ruwa kamar da bakin kwarya na tsawon lokaci a Kano, ana ganin lamarin na da alaƙa da ruwan.

Kano – Wani matashi ɗan shekara 25 a duniya, Ghaddafi Saleh, ranar Laraba, an tabbatar da ya rasu jim kaɗan bayan tsamo shi daga cikin kwata cikin mawuyacin hali.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, ne ya tabbatar da faruwar hakan a wata sanarwa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kakakin hukumar ya ce:

“A yau Laraba 20 ga watan Yuli, 2022, mun samu wani kiran gaggawa daga Malam Abdulƙadir, da misalin ƙarfe 7:26 na safe. Ya faɗa mana cewa wani mutumi ya faɗa Kwata a yankin Tarauni, kan hanyar Zariya.”

Wane mataki suka ɗauka bayan samun rahoton? Bayan samun wannan rahoton, Abdullahi ya ƙara da cewa nan take suka haɗa tawagar jami’ai da ke kan aiki kuman sun dira wurin da misalin ƙarfe 7:34.

Da zuwansu a cewar kakakin hukumar kashe gobaran, suka gano wani mutum da bai wuce shekara 25 ba mai suna, Ghaddafi Saleh, a cikin Kwata.

Abdullahi ya ce mutumin, wanda aka tsamo cikin mawuyacin hali, ya ƙarisa rasuwa daga baya kuma tuni aka miƙa gawarsa ga Insufecta Bashir Abdullahi na caji ofis ɗin hanyar Zariya.

Meyasa hadda faɗawar matashin cikin kwata?

Bayanai sun nuna cewa ana tsammanin mamakon ruwan da aka tafka ranar Lahadi ne ya rutsa da matashin, inda ya faɗa babban hanyar ruwa kuma ya maƙale.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here