2023: Matashi Mai Shekaru 35 Daga Jahar Kano Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa
Wani matashi daga jahar Kano ya gana da makusanta Ganduje domin sanar dasu aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.
Matashin ya bayyana balo-balo cewa, zai tsaya takarar shugaban a karkashin inuwar jam’iyyar APC a zaben 2023.
Sai dai, wasu matasan sun bayyana goyon bayansu ga gwamnan jahar Bauchi, inda suke neman shi ma ya tsayawa takarar.
Wani matashi dan shekaru 35 da ke neman tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC a jahar Kano, Malam Aminu Sa’idu, a jiya ya gana da mataimaka na musamman (SAs) ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje don sanar da su burinsa.
Da yake magana da Daily Trust bayan ganawar, matashin ya ce yana daga cikin shawarwarin da yake bi gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Read Also:
Ya kuma ce ganawar ta yi daidai da kudirin dake rajin ba matasa damar a dama dasu a mulki na”Not Too Young to Run”, da kuma dabarun fadada aniyarsa zuwa dukkan sassan kasar.
Wata kungiya ta yi kira da a mika Najeriya ga gwamnan jahar Bauchi, Bala Mohammed
Amma wata kungiyar matasan Arewa a karkashin inuwar kungiyar Concerned Citizens Like-Minds (CCLM) ta ce Gwamna Bala Mohammed na jahar Bauchi shi ne mafi cancanta wajen tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, jaridar Sun ta ruwaito.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a Kaduna, kakakin kungiyar, Kwamared Mujaheed Amin-Modibbo, ya ce:
“Sanata Bala ya nuna halaye na kwarai na nagartaccen shugaba tun lokacin da ya fara siyasa a Najeriya tun daga asalinsa, a matsayin minister a FCT sannan a matsayin Gwamna na yanzu na jahar Bauchi.”
Kungiyar ta nemi gwamnan ya tsaya takarar shugaban kasa; yakin neman zabe da karfi, lashe zaben tare “dawo da” martabar kasar.