Gwamna Matawalle ya Haramta wa Sarakunan Jiharsa Naɗa Sarauta

 

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya haramta wa Sarakunan jihar naɗa kowane mutum sarauta har sai sun samu izini.

A makon da ya gabata ne Najeriya ta ɗau zafi bayan masarautar Yandoto a Zamfara ta naɗa kasurgumin ɗan bindiga Sarauta.

Tuni gwamnatin Zamfara ta soke nafin sarautar kuma ta ɗauki mataki domin kare faruwar irin haka nan gaba.

Zamfara – Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci baki ɗaya masarautun jihar da su nemi sahalewar gwamnati kafin naɗa wa wani rawanin Sarauta.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da babban mai taimaka masa ta ɓangaren yaɗa labarai, Zailani Bappa, ya fitar, kamar yadda rahoton Daily Trust ya tabbatar.

A rahoton Channels tv, gwamna Bello Matawalle ya ce:

“Baki ɗaya Sarakuna, manyan hakimai da hakimai da ke faɗin jiha, muna umartan su da su nemi izinin gwamnatin jihar kafin naɗa wa kowane mutum rawanin sarauta.”

“Wannan matakin ya zama wajibi domin sa ido kan naɗin sarautar da ake yi ba tare da la’akari ba da kuma yuwuwar zubar da ƙimar masarautu.”

“Saboda haka daga yanzu, babu wani Sarki, babban Hakimi ko Ƙarami da zai naɗa ko waye wani muƙamin sarauta ba tare da samun sahalewa da amincewa a hukumance daga gwamnatin jiha ba.”

Wane hukunci gwamnati ta tanda ga masu kunnen ƙashi?

Bugu da ƙari, gwamnan ya ƙara da gargaɗin baki ɗaya sarakunan jihar cewa bin wannan umarni ya zama tilas kuma duk wanda ya yi kunnen gashi zai ga abinda zai biyo baya.

“Biyayya ga wannan umarnin ya zama tilas kuma duk wanda ya tsallake shi gwamnati zata tsawatar masa tsawa ta gaske.”

Legit.ng Hausa ta rahoto muku yadda masarautar Yandoto ta naɗa ƙasurgumin ɗan ta’adɗa, Adamu Aleru, wata sarauta, lamarin da ya ta da ƙura a ciki da wajen jihar Zamfara.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here