Gwamna Matawalle ya Raba wa Sarakunan Gargajiya da ke Jaharsa Manyan Motocin Alfarma 260

Gwamnan Jihar Zamfara a arewacin Najeriya, Bello Matawalle, ya raba wa sarakunan gargajiya da ke jihar manyan motocin alfarma.

Rahoton da kafar Channels TV ta ruwaito ya ce Sarkin Musulmi na Najeriya Sa’ad Abubakar III ne ya raba motocin 260 a gidan gwamnatin Zamfara.

Gwamnan ya ce an raba motocin ne saboda muhimmancin sarakuna a cikin al’umma da ke a matsayin “turakun al’adu da addini”.

“Mun yanke shawarar ba su sabbin motocin ne saboda yadda gwamnatina ke mutunta sarakunan gargajiya,” in ji shi. “Mun raba wa sarakuna 17, da manyan hakimai 13, da kuma hakimai 230 a faɗin jihar.”

Kazalika, gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa kai da sarakunan da kuma shugabannin addini don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a jihar.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here