Wasu su na Ganin Matsalar Rashin Tsaro Dama ce da Zasu ci da Siyasa, su Rika Kawo Shirman Shawarwarin da ba Zasu Kai ko Ina ba – Gwamna El-Rufai ga Atiku Abubakar
Ra’ayin Gwamna Nasir El-Rufai ya sha banbam da na Atiku Abubakar.
Atiku ya bada shawara a tura Sojoji su tsare duka makarantun Najeriya.
Gwamnan ya yi watsi da wannan shawarar, ya ce ba mai bullewa ba ce.
Gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana game da shawarar da Atiku Abubakar ya bada na aika sojoji domin su tsare dalibai a Najeriya.
Malam Nasir El-Rufai ya yi kaca-kaca da shawarar da aka ba gwamnati, ya ce Najeriya ba ta da karfin da za ta iya kai sojoji zuwa kowace makaranta.
Kamar yadda JJ Omojuwa ya wallafa a shafinsa na Twitter, Gwamnan ya bayyana haka ne a wani bidiyo inda aka yi masa tambaya game da lamarin tsaron.
Read Also:
Ya ce: “Ba mu da isassun jami’an tsaro, ina ganin zai fi kyau muyi amfani da kayan yakinmu wajen maganin miyagun da akasari su ke kungurmin jeji.”
“Sai mun jira sun zo makarantu sun kama ‘ya ‘yanmu? Sojoji nawa za ka baza a makarantu su tsare ‘yan bindiga 200 da za su zo a lokaci daya su kai hari?”
“Sojoji nawa gare mu? Jami’ai nawa za su rika aiki a Arewa maso gabas da Arewa maso yamma, nawa za ka kai jahar Kaduna inda mu ke da makarantu 300.”
Ba zai yiwu ba. Wasu su na ganin wannan matsalar rashin tsaro dama ce da za su ci da siyasa, su rika kawo shirman shawarwarin da ba za su kai ko ina ba.”
“Ban yarda da wannan ba, miyagun ‘yan bindiga ne, marasa gaskiya ne, wanda mafi yawancinsu su ke jeji, mu gano su, mu je mu yi maganinsu.” Inji El-Rufai.
Gwamnan yake cewa bayan an lallasa mafi yawan ‘yan bindigan, za a iya zama da ragowar da su ka tuba, sai ayi masu afuwa, kamar yadda wasu ke fada.