Yadda Kungiyar Maza Masu Rowa ta Bunkasa a Sauran Kasashen Afirka
Kungiyar samari masu masu matse aljihu ta fara bunkasa zuwa sauran kasashen Afirka.
Wasu daga cikin kasashen da suka bude rassan kungiyar sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.
A ranar Litinin ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a dandalin sada zumunta na Twitter.
Kungiyar maza masu rowa da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.
A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.
Read Also:
Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.
Samari da dama sunyi ta fitowa suna nuna goyon bayansu ga kungiyar da manufofinta inda wasu suka rika wallafa katin shiga kungiyar da matsayinsu a shafukansu.
Wasu daga cikin manyan mawakan Najeriya suma ba a bar su a baya ba wurin shiga kungiyar cikinsu akwai mai kamfanin waka ta Mavin Records, Don Jazzy.
Shima mawaki Mr Eazi dan asalin Najeriya amma mazaunin Landan ya wallafa kattinsa na shaidar zama da kungiyar samarin masu rowa a shafinsa na Twitter.
Mutane da dama sun yi ta yi wa juna barkwanci tare da yin nishadi game da kafuwar kungiyar da yadda zata sauya alakar ‘yan mata da samarinsu.