Ministan Kula da Ayyukan Agaji na Kasar Rasha ya Rasa Ransa Garin Ceto Mai ɗaukar Hoto

 

Ministan da ke kula da ayyukan agajin gaggawa na Rasha Yevgeny Zinichev ya mutu yayin wani atasaye da ake yi a yankin Arctic mai tsananin sanyi na arewacin duniya.

Ma’aikatarsa ta ce hatsarin ya auku ne lokacin da Mista Zinichev ya yi kokarin ceto ran wani mutum a yankin Norilsk.

Wani rahoton tashar talabijin ta kasar, wato RT ya ce ya mutu ne yayin da ya yi kokarin ceto wani mai daukan hoto wanda ya fado daga saman wani dutse yayin da ministan ke tattaunawa da manema labarai.

Kakakin ma’aikatar Margarita Simonyan ta ce ministan ya garzaya domin taimaka wa mutumin amma sai ya fada kan wani dutse mai tsini wanda ya yi ajalinsa take.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here