Yi wa Mata Fyade a Tigray: Ministar Mata ta Habasha ta yi Murabus

 

Ministar mata ta Habasha ta yi murabus tana mai cewa ba ta shirya bata tarihinta ba.

Filsan Abdullahi Ahmed ita ce jami’ar gwamnatin kasar ta farko da ta amince cewa an yi wa mata fyade a yankin Tigray da ke fama da yaki.

A watan da ya gabata, ta ce tana fatan jami’an tilasta bin doka za su yi hanzarin gano wadanda suka aikata laifin da kuma girman cin zarafin mata ta yadda za a yi adalci.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun zargi sojojin Habasha da kawayensu na Eritrea da yi wa daruruwan mata da ‘yan mata fyade a Tigray.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here