Wani Daga Cikin Ministocin Buhari ya Fashe da Kuka

A Calabar, jihar Cross River, matasa sun lalata dukiyoyin gwamnati da dama da ke jihar

Wannan al’amarin ya sa karamin ministan wutar lantarki, Goddy Agba, zubar da hawaye  Inda yayi kira ga matasa da su ajiye makamansu, za a yi duk abubuwan da suke so Hawaye sun kubce wa Goddy Jeddy Agba, karamin ministan wutar lantarki, a ranar Talata, 27 ga watan OKtoba, yayin da yake zagayen duba asarorin da matasa suka tafka wa Calabar, babban birnin jihar Cross River.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Agba ya fashe da kuka, bayan ganin irin aika-aikar da bata-gari suka yi a asibitin masu tabin hankali, inda suka lalata tsadaddun abubuwa. Gwamna Ayade, ya bayyana irin dumbin dukiyar da jihar Cross River ke bukata don gyara duk abubuwan da aka bata

Ministan ya duba ofisoshin gidan talabijin na NTA, na WAEC da sauran wurare. Ya bai wa matasa hakuri a madadin gwamnatin tarayya, inda yace ya fahimci irin radadin da suke ji, kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari zai duba bukatunsu. A cewarsa, “Na yi matukar mamakin irin asarar da muka tafka, daga dukiyoyin har matasan duk namu ne, wajibi ne mu taru mu gyara. Muna bai wa matasa hakuri a kan radadin da suka ji da har ya kai su ga lalata wadannan dukiyoyin, mun fahimcesu kuma za mu gyara.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here