Motar Kwastam ta Kashe Mutane 5 yayin Bin Fasakwaurin Shinkafa a Jahar Katsina
Wata motar kwastam ta kucce ta yi kan jama’a yayin da ta biyo yan fasa kwauri a garin Jibia dake jahar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin da ya afku ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 5 tare da jikkata wasu da dama.
Mazauna garin sun fito zanga-zanga don nuna fushinsu kan abinda ya faru, matasa sun kone motar kwastam.
Jibia, Katsina – Mutane sun fito zanga-zanga a garin Jibia, jahar Katsina, kan kashe wasu mutum 5 da jami’an kwastam suka yi yayin da suka biyo masu fasakwaurin shinkafa.
Read Also:
Wasu shaidu sun bayyana cewa mutane da dama sun samu jikkata kuma a halin yanzun suna gadon asibiti ana kulawa da lafiyarsu.
Shaidun sun tabbatar da cewa wata motar jami’an kwastam ce ta yi kan dandazon mutane yayin da suka biyo wasu da ake zargin yan fasa kwaurin shinkafa ne a yankin.
Lamarin yayi sanadiyyar mutuwar mutun 5 nan take yayin da wasu da dama suka ji raunuka.
Me ya jawo hatsarin?
Wata majiya da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa jaridar Premium times cewa:
“Sun biyo yan fasa kwauri cikin matsanancin gudu, direban ya kasa sarrafa motar ta yi cikin jama’a inda ta hallaka mutum biyar. Wannan shine dalilin zanga-zanga.”
“Fusatattun matasa dake cikin masu zanga-zangar sun yi kaca-kaca da motar jami’an kwastam din.”