Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya Aiko da Sakon Ta’aziyyarsa na Rashin Hajiya Maryam Ado Bayero

 

Muhammadu Sanusi II ya yi magana a kan mutuwar Maryam Bayero.Sanusi II ya aiko da sakon ta’aziyyarsa, ya na cewa an yi babban rashi.

Tsohon Sarkin Kano ya yi wa Mai babban dakin addu’o’i ne a karatunsa.

Legi.ng Hausa ta samu labari cewa tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya aiko sakon ta’aziyyarsa na mutuwar Hajiya Maryam Ado Bayero.

A wani bidiyo da yake yawo a dandalin sada zumunta na zamani, Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana game da babban rashin da aka yi a Kano.

Da yake jawabi a jiya, Sanusi II ya ce: “Yau mun tashi da rasuwar mahaifiyarmu, Maryam Bade (Ado Bayero), uwargidar marigayi Sarki Ado Bayero.”

Mai martaban ya cigaba da cewa:

“Ta rasu a kasar Masar, mu na mika ta’aziyya ga daukacin al’umma.” A wannan bidiyo da wani mai suna Kwankwason Twitter ya wallafa a shafinsa, Muhammadu Sanusi II ya yi wa marigayiyar addu’a tare da sauran jama’a.

“Allah ya sa ta huta, Allah ya sa ciwon da ta yi ya zama kaffara.” Sanusi ya ke cewa za ayi rashin mahaifiyar magajinsa da kuma Sarki Nasiru Ado Bayero.

Malam Sanusi II wanda ya bar karagar mulki a bara ya sa an yi wa marigayiyar salatin Annabi SAW kafa 10 da karatun suratul Ikhlas domin ta samu ceto.

Mai martaban wanda ya rike kujerar gwamnan babban bankin Najeriya na CBN ya kira Hajiya Maryam Ado Bayero wanda ta rasu a ranar Juma’ar nan.

A karshe bayan tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi wa Mai babban daki addu’a, ya kuma yi addu’a ga sauran wadanda su ka riga mu cika wa.

Sarauniya Maryam Ado Bayero ta bar Duniya ne bayan kusan shekaru bakwai da mutuwar Ado Bayero.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here