Karbar Rashawa: Yadda Mukaddashin Kwanturola na Hukumar Shiga da Fice ta Kasa ya Kame Jami’ansa
Mukaddashin Kwanturola na hukumar shige da fice ta kasa ya kame jami’ansa na aikata karbar rashawa.
Ya bayyana cewa, ya dura ofishinsu, inda suka nemi ya biya makudan kudade ba bisa ka’ida ba.
Ya bayyana cewa, gani ya kori ji, domin kuwa ya tabbatar da zargin da ake yi wa jami’an hukumar.
Mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS), Isa Jere Idris, ya cafke wasu jami’an hukumarsa dumu-dumu a kokarinsu na hada harkallar badakala.
Idris wanda ya yi shigar burtu a matsayin mai neman fasfo na kasa da kasa a a ofishin rundunar da kejihar Legas, ya kama su lokacin da suka yi masa tayin taimaka masa wajen siyan fasfo din ta hanyar da bata dace ba.
Mukaddashin Kwanturolan ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da jaridar Premium Times.
Read Also:
Ya ce ziyarar ta ba zata a Ikoyi ita ce ta tabbatar da zargin da ake yi wa jami’an ofisoshin shige da fice na jahar Legas da suka hada da Ikoyi, Ikeja da garin FESTAC.
Ya ce lokacin da ya tuntubi jami’an a ofishin na Ikoyi, an ba shi farashi daban-daban na fasfo.
Ya shaida wa Premium Times cewa:
“Lokacin da na tunkari jami’an, sun ba ni jadawalin farashi ba tare da sun gane ni ba. Sun ce fasfo mai shafuka 32 na tsawon shekaru biyar zan kashe N45,000 maimakon N27,000.
“Sun ce mai shafuka 64 na shekaru biyar zan kashe N55,000 maimakon N37,000, da N95,000 ga fasfo mai shafuka 64 na shekaru 10 maimakon N72,000.
“An tambaye ni daga ina na ce Jahar Neja. Sun kuma tambaye ni idan ina da shaidar zama dan kasa da sauran takardu kuma na ce ba ni da daya. Don haka suka ce za su karbi Naira dubu uku da dari biyar domin su samar min da dukkan takardun.”
Duk da haka, ya ce har yanzu jami’an ba su san ko wanene shi ba, kuma kwanturolan hukumar na Legas, Bauchi Aliyu, ya yi mamakin lokacin da ya bayyana a ofishinsa.