Kamfanin MultiChoice na Duba Yuwuwar Yin Wasan Kwaikwayo Kan Uwargidan Shugaba Buhari, Aisha Buhari
Kamfanin nishadantarwa da ke karkashin MultiChoice, Africa Magic, ya na duba yuwuwar yin wasan kwaikwayo kan Aisha Buhari.
 Kamar yadda shugaban kamfanin ta Najeriya, Busola Tejumola ta sanar, su na shirin yin fim kan uwargidan shugaban Buhari.
 Kamfanin ya yi wani taron baje-koli ne a jahar Kano na kwana biyu inda sama da furodusoshi dari biyu suka halarta.
Kano – Africa Magic, gagarumin kamfanin nishadantarwa mallakin MultiChoice, su na duba yuwuwar yin wasan kwaikwayo kan Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Daily Trust ta rawaito cewa, Busola Tejumola, shugaban tashar ta Najeriya, ta bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ta ke jawabi a taron kwana biyu da Africa Magic ta shirya na baje koli a jahar Kano, wanda aka kammala jiya.
A takardar da MultiChoice ta fitar, taron da ta shirya an samu ya hade da taron shekara- shekara na kungiyar watsa labarai na Najeriya, BON, ya samar da dama ga furodusoshi wurin mu’amala kai tsaye da Africa Magic domin samun damar tallatawa da siyar da hajojinsu.
Taron wanda ya samu halartar sama da furodusoshi dari biyu daga arewacin Najeriya, na son samar da hanyar samun riba da nasara ga dukkan masu ruwa da tsaki, Tejumola tace.
“Kasuwar baje kolin Africa Magic hanya ce da aka kirkiro wanda muke fatan zai samarwa da kowanne furodusa damar mu’amala da masu siya. Zai samar mana da damar mu’amala da furodusoshi domin gane yanayi da ingancin abinda suka kawo..
“Babu shakka wannan aikin zai kai mu kusan dukkan sassan kasar nan. Lokaci ya yi da arewa za ta sanar da duniya labarin ta. Babu wani lokaci da ya fi dacewa da ya wuce yanzu,” tace.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here