Musabbabin Abinda ya Kashe Mutane 7 Jahar Osun
Ƴan sanda a jahar Osun sun tabbatar da mutuwar mutum bakwai ƴan gida ɗaya sakamakon shaƙar iska mai guba.
Rundunar ƴan sandan Osun ta ce mutum takwas aka samu kwance a ɗakunansu a gidan da suke amma mutum ɗaya aka samu yana numfashi.
Read Also:
Kakakin ƴan sandan jahar Yemisi Opalola ta shaida wa BBC cewa makwabta ne suka fara fahimtar al’amarin waɗanda suka yi tunanin dukkaninsu sun mutu.
Ta ce ƴan sanda na gudanar da bincike kan musabbabin al’amarin.
Jami’ar ƴan sandan ta ce hayaƙin janareto na iya kasancewa musabbabin kisan.
Article share tools