Mutane 25 Sun Mutu a Harin da Matasan Irigwe Suka Kai wa Musulmai Matafiya 90 Hari a Jahar Plateau
Kakakin ‘yan sanda Jos yace ana zargin matasan Irigwe (yawancinsu Kirista) suka kaiwa Musulmai 90 hari .
Jami’in dan sandan ya ce an damke mutum shida cikin maharan Akalla mutum 25 suka mutu yanzu, cewar gwamnatin jahar da Miyetti Allah.
Wasu yan bindiga da ake zargin matasan Irigwe ne sun kai wa Musulmai matafiya 90 hari a jahar Plateau ranar Asabar, akalla mutum 25 sun mutu, ‘yan sanda suka tabbatar.
Kakakin hukumar yan sandan jahar, Ubah Ogaba, ya bayyana cewa wasu matasa Kirista yan garin Irigwe suka kaiwa Musulman farmaki, rahoton Channelstv.
A cewarsa:
“Misalin karfe 0928hrs, hukumar yan sandan jahar Pleatuea ta samu labarin cewa wasu mahara da ake zargin matasan Irigwe ne (yawancinsu Kirista) sun kai hari kan motocin Musulmai biyar.”
“Mutum ashirin da biyu aka kashe yayinda 14 suka jikkata.”
Jami’in yan sandan ya kara da cewa mutum 21 sun tsallake rijiya da baya.
Wani jami’in gwamnatin jahar ya bayyanawa Channels cewa adadin wadanda aka kashe ya fi haka.
Read Also:
Jami’in gwamnatin mai suna Danladi Atu wanda ya ziyarci asibitin da aka kai wadanda suka jikkata yace:
“Mutum 25 aka tabbatar yanzu sun mutum.” Hakazalika kungiyar Miyetti Allah MACBAN tace ta kirga gawawwaki 25.
Wakilin Miyetti Allah, Malam Nura Abdullahi yace:
“Mun yiwa gawawwaki 25 wanka kuma muna shirin binnesu.”
Gwamnan Plateau, Simon Lalong, ya yi Alla-wadai da wannan hari.
A cewar mai magana da yawunsa, Makut Simon Macham, yace:
“An tura jami’in tsaro wajen.” Hukumar yan sanda yace an damke mutum shida an an kwatar da kuran.
Binne Mamatan
An yi jana’izar matasan da halarci taron Zikirin kasa a jahar Bauchi 25 da yan bindigan kabilar Irigwe suka hallaka a Gada-biyu, karamar hukumar Jos ta Arewa a Jahar Plateau.
An binne mamatan ne a makabartar Dadinkowa da cikin jahar, rahoton Daily Nigerian.
Jami’in gwamnatin mai suna Danladi Atu wanda ya ziyarci asibitin da aka kai wadanda suka jikkata yace mutum 25 aka tabbatar yanzu sun mutu.
Hakazalika kungiyar Miyetti Allah MACBAN tace ta kirga gawawwaki 25. Wakilin Miyetti Allah, Malam Nura Abdullahi yace:
“Mun yiwa gawawwaki 25 wanka kuma muna shirin binnesu.”