Cutar Sarkewar Numfashi: Adadin Mutanen da Suka Kamu da Cutar Ranar Talata

 

Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara.

Kusan makonni uku a jere, yan Najeriya sama da 1000 ke kamuwa da Korona kullum.

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar hana fita idan adadin ya cigaba da karuwa.

A ranar Talata, 27 ga watan Junairu 2021, Mutane 1,303 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Daga cikin wadanda aka sallama, akwai mutane 542 da sukayi jinya cikin gidajensu a Legas, 103 a Plateau da 22 a jihar Kwara.

Abin takaici, mutane 15 sun rasa rayukansu. Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 124,299 a Najeriya.

Daga cikin mutanen da suka kamu, an sallami 99,276 yayinda 1,522 suka rigamu gidan gaskiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here