Mutane 7 da Ake Hasashen za su Maye Gurbin Ngelale
Wasu sun fara bayyana wadanda suke ganin Shugaba Tinubu zai iya yin amfani da su a mukamin mai magana da yawunsa.
Wa zai canji Ajuri Ngelale?
Ngelale ya ajiye mukamin kakakin shugaban ne a ranar Asabar 7 ga watan Satumbar 2024 saboda dalilin kula da rashin lafiyar iyalansa.
Legit Hausa ta leko wadanda ake tunanin za su iya maye gurbin Ngelale:
1. Daniel Bwala
Daniel Bwala shi ne tsohon hadimin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a zaben 2023.
Daga bisani ya watsar da Atiku inda ya koma goyon bayan Tinubu a fili wanda ya sa ake tunanin shugaban zai iya saka masa da mukamin.
2. Bayo Onanuga
Bayo Onanuga shi ne wanda ke rike da mukamin hadimin shugaban bangaren yada labarai da tsare-tsare.
Onanuga shi ne tsohon daraktan hukumar NAN yana da kusanci da Tinubu da ake ganin zai iya ba shi mukamin.
3. Tolu Ogunlesi
Read Also:
Tolu Ogunlesi ya kasance daga cikin wanda ake sa ran za su samu mukamin kakakin Bola Tinubu bayan ajiye aiki da Ngelale ya yi.
Ogunlesi shi ne tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bangaren sadarwa ta zamani.
4. Sunday Dare
Tsohon Ministan wasanni a mulkin Muhammadu Buhari, Sunday Dare na cikin wadanda ake sa ran su gaji mukamin Ngelale.
An yi ta hasashen bayan Tinubu ya dare mulki zai nada Dare mukamin Minista amma hakan bai yiwu ba.
5. Tunde Rahman
A yanzu haka Tunde Rahman shi ne hadimin Tinubu a bangaren sadarwa bayan ya rike mukamin ga shugaban kafin a zabe shi.
6. Temitope Ajayi
Kaman Tunde, shi ma Ajayi hadimi ne ga Bola Tinubu a bangaren sadarwa da yada labarai.
Ajayi ya yi aiki da Tinubu tun lokacin kamfen zaben 2023 wanda ya dade tare da shugaban a bangaren sadarwa.
7. Otega Ogra
A watan Yulin 2023, Shugaba Bola Tinubu ya nada Ogra a matsayin hadiminsa a bangaren sadarwa ta zamani.
A baya, Ogra ya yi aiki a bankunan Najeriya kafin ya koma aiki da kamfanin BUA na Abdussamad Rabiu.