Mutane 13 Sun Mutu a Harin Bom a Somaliya

Aƙalla mutum 3 ne suka mutu a wani harin bom da aka kai tsakiyar Somaliya.

‘Yan sanda sun ce wata motar ɗaukar kaya ce ɗauke da abubuwan fashewa ta tarwatse a shingen binciken ababen hawa a garin Baldwin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji da fararen hula.

Harin ya kuma jikkata gomman fararen hula tare da lalata gine-ginen da ke kusa da wurin.

Kawo yanzu ba a san wanda ke da alhakin harin ba, sai dai ƙungiyar al-Shabab ta sha kai makamantan waɗannan hare-hare a ƙasar.

Kungiyar ta shafe fiye da shekar 10 tana yaƙi da gwamnatin ƙasar, a ƙoƙarin da take yi na kafa gwamnati mai bin tsarin shari’ar musulunci.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com