Mutane 30 Sun Mutu a Harin da Isra’ila ta Kai wa Gaza

 

Ma’aikatar lafiya a Gaza karkashin ikon Hamas ta ce an kashe mutane aƙalla 30, an kuma jikkata sama da 100, a wani hari da Isra’ila ta kai wata makaranta ɗauke da ɗaruruwan Falasɗinawa da aka ɗaiɗaita.

Sojojin Isra’ila sun ce sun kai harin ne kan cibiyar Hamas da ke cikin ginin makarantar a yammacin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza.

Tun da farko, sojojin sun yi gargaɗin cewa dole ta sa za a rage kwashe mutane a kusa da birnin Kha Younis saboda ƙaruwar barazanar mayaka da kuma harin rokoki.

Ita ma ma’aikatar tsaron Isra’ila (IDF) ta yi irin wannan gargaɗi a makon da ya gabata.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here