Mutane 7 Sun Rasa Rayukansu Sanadiyyar Hatsarin Mota a Kan Hanyar Lambata Zuwa Minna
Hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane 7 a kan hanyar Lambata zuwa Minna.
Hatsarin ya faru da safiyar yau Alhamis, 22 ga watan Yuli mintoci kadan bayan karfe bakawai.
An ruwaito cewa, ganganci da gudun wuce gona da iri na direbobin ne ya jawo mummunan hatsarin Mutum bakwai sun mutu, a safiyar ranar Alhamis, a wani mummunan hatsarin mota wanda ya faru a hanyar Lambata zuwa Minna, jahar Neja, Daily Trust ta ruwaito.
Read Also:
Hatsarin, a cewar kwamandan sashin kula da hadurra (FRSC), Musa Muhammed, ya faru ne a kauyen Dagibe ‘yan mintoci kadan bayan karfe 7 na safe.
Hatsarin ya rutsa da motoci biyu, wata mota kirar Mazda 323 mai lamba kamar haka CRC686XN da kuma wata motar golf ta Volkswagen mai lamba KTU506BK.
Jami’an hukumar FRSC ba su iya tantance ko su wanene wadanda lamarin ya rutsa da su ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton amma maza shida da mace daya sun mutu.
Wannan mummunan hatsarin ya yi sanadin raunata maza biyu.
Bayanai sun ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudu na wuce gona da iri da kuma rashin kulawar da direbobin ke yi.
Wadanda suka jikkata, a cewar Muhammed, an kai su Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Gawu Babangida yayin da aka kai gawarwakin dakin ajiyar gawarwakin na Sabon Wuse.