Mutane 6 Sun Shiga Hannu Kan Zambar Mutane a Shafin Masu Auren Jinsi ɗaya

 

Ƴan sandan jihar Nasarawa a arewa ta tsakiyar Najeriya sun kama mutum shida da ake zargin suna amfani da wani shafin intanet suna zambar mutanen da suke auren jinsi ɗaya.

An ce waɗanda ake zargin suna amfani da shafin ne don neman amincewar mutane kafin daga bisani su zambe su.

Kamen ya zo ne bayan wani da abun ya shafa ya ce an ɗauki hotunan tsiraicinsa, kuma an yi masa barazanar yaɗa hotunan idan bai ba da kuɗi ba

An ce lamarin ya faru ne a unguwar Masaka, a ƙaramar hukumar Karu da ke da iyaka da birnin tarayya Abuja.

Kakakin ƴan sandan jihar, Ramhan Nansel ya gaya wa BBC cewa wanda ake zargin, maza huɗu da mata biyu, sun yaɗa hotunan masu neman auren jinsi ɗaya, kuma sun gayyaci masu sha’awar yin haka don shirya ranakun da za su haɗu.

Sannan kuma sai su zambaci mutanen ko su ƙwace musu ƙadarorinsu kuma su yi musu barazanar ɓata musu suna don rufe bakinsu.

Ƴan sandan sun ce za a yanke wa waɗanɗa ake zargin hukunci bayan kammala bincike.

Gwamnatin Najeriya ta hana auren jinsi ɗaya, ta kuma saka dokar ɗaure mutum har na shekaru 14 idan an kama masu aikata laifin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here