Ku Biya N250,000 Don Mayar da Motocinku Kan Amfani da Iskar Gas Maimakon Fetur-Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta yi bayanin cewa yan Najeriya da suka mallaka mota zasu biya N250,000 domin a mayar musu da motocinsu masu amfani da iskar Gas maimakon man fetur.

A ranar Talata, Shugaban kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Mele Kyari, ya ce za’a mayarwa masu motoci milyan daya kyauta.

Amma yayin hira da shirin Sunrise Daily na tashar Channels TV ranar Laraba, Justice Derefaka, mai bada shawara ga karamar ministan mai kan harkallar iskar Gas, Timipre sylva, ya yi bayanin cewa ba kyauta bane, mutane zasu biya kudi.

“Kudin da za’a biya ya danganta da irin motar da tukunyar Gas din za tayi amfani. Ga masu manyan motoci SUV, ya fi girma kuma za’a biya kimanin N200,000 zuwa N250,000 kuma yana fin hakan idan tukunyar motar shida ne, ”

Ya kara da cewa bai zama dole a biya dukkan kudin lokaci guda ba, mutum zai iya biya cikin watanni biyar zuwa bakwai.

“Kuma a haka, zai rage shan man ka da kimanin kashi 45 zuwa 50. Saboda haka ya fi sauki, ” ya kara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here