Sama da N345m Sun ɓata a Asusun Babbar Kotun Shari’a a Jahar Kano
A gidan adalci, an yi awon gaba da kimanin N350m a jahar Kano.
An kai karar wannan lamari wajen hukumar yaki da rashawa.
Shugaban kotunan Shari’a yace kudaden gado ne da aka kai kotu don rabawa.
Kano – Kudi Sama da N345million sun yi batan dabo daga asusun babbar kotun Shari’a a jahar Kano, a cewar rahoton gidan rediyon Freedom.
Babban Alkalin kotun Shari’ar jahar Grand Khadi Tijjani Yakasa ya tabbatar da hakan inda yace an kai karan lamarin ofishin sauraron kararraki da yaki da rashawa na Kano domin bincike.
Read Also:
Sakataran kotun, Haruna Khalil, ya bayyana cewa tuni an kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike kan lamarin.
A cewarsa, kudin da suka bata kudaden gadon mutane ne da aka ajiye a hannun kotun domin rabawa masu hakki.
Yace an gano kudaden sun yi batan dabo ne yayinda akayi kokarin cire wasu kudade, kawai sai aka ga milyan 9 kawai suka rage a asusun.
An sace kwamfutoci don tsegumi ga bincike
An tattaro cewa bayan nada kwamitin bincike, an sake sace wasu kwamfutoci daga kotun don kawo cikas ga bincke.
A cewar shugaban hukumar yaki da rashawa a hukumar Kano, Mahmud Balarabe, yace an gayyaci dukkan wadanda suke da hannu, ciki har da ma’aikatan banki.