Gwamnatin Tarayya ta Nada Sababbin Sakatarori a Ma’aikatun NBTE, NSSEC da NCCE

 

Shugaban kasa ya amince da nadin sababbin shugabannin ma’aikatun Gwamnati.

Ma’aikatar ilmi ta ce an nada sakatarori a ma’aikatun NBTE, NSSEC, da ta NCCE.

Farfesa Idris Bugaje, Abdullahi Abba, da kuma John Enaohwo sun samu kujeru A ranar Laraba, 14 ga watan Afrilu, 2021 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da wasu nadin mukamai a ma’aikatar ilmi ta tarayya.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa shugaban Najeriyar ya yi nadin mukaman ne a ma’aikatun NBTE, NSSEC, NCCE da kungiyar UNESCO.

Sanarwar da ta fito daga ma’aikatar ilmi ta ce shugaban kasa ya nada Farfesa Idris Muhammad Bugaje a matsayin babban sakataren ma’aikatar NBTE.

Idris Muhammad Bugaje wanda ke shugabantar makarantar Kaduna Polytechnic ya zama shugaban ma’aikatar da ke kula da makarantun fasaha.

Kamar yadda mai magana da yawun bakin ma’aikatar ilmin tarayya, Ben Goong, ya bayyana, Dr. Benjamin Abakpa ya zama shugaban ma’aikatar NSSEC.

Har ila yau gwamnatin tarayya ta nada Farfesa Paulinus Okwelle a matsayin babban sakataren hukumar NCCE mai kula da makarantun horas da malamai.

Shi kuma Farfesa John Enaohwo shi ne wanda zai lura da majalisar da ke kula da aikin NCCE.

Sanarwar ta ce Farfesa Abdullahi Abba ya zama sabon shugaban majalissar da ke kula da babbar jami’ar kiwon lafiya ta tarayya da ke garin Otukpo, Benuwai.

Ben Goong a madadin Ministan ilmi na tarayyar Najeriya, ya ce wadanda aka ba wadannan mukami za su fara aiki a ranar Juma’a 16 ga watan Maris, 2021.

Shi kuma Farfesa Ibrahim Muhammad ya zama Darekta a cibiyar harshen larabci da ke Ngala, yayin da Hajo Sani ta zama wakiliyar Najeriya a kungiyar UNESCO.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here