Labarin Naɗin Sarautar Sarkin Shuwa Arab a Jahar Edo ya Haifar da Tashin Hankali a Jahar

 

Zafafan kalamai sun biyo bayan shirin da wata kabila daga Borno ke yi na nada daya daga cikin membobinta a matsayin Sarkin Shuwa Arab.

Wasu mazauna birnin Benin sun bayyana dalilin da ya sa ba za su bari a gudanar da bikin da aka shirya ba.

Oba na Benin shi ne Sarki kuma mai kula da al’adun kuma shi aka sani a matsayin babban basarake a garin Benin.

Birnin Benin, jahar Edo – Wasu kungiyoyi a jahar Edo sun yi watsi da shirin da wata kabila daga Borno na nada Idris Adanno a matsayin Sarkin Shuwa Arab na jahar Edo.

PM News ta ba da rahoton cewa labarin nadin sarautar da aka shirya yi a ranar Asabar, 21 ga watan Agusta, a wani yanki na birnin Benin, ya haifar da tashin hankali a jahar.

Mazauna birnin sun sha alwashin cewa ba za su bari a yi wannan nadin sarautar ba. Katin gayyatar bikin nadin sarautar, wanda aka gani a Facebook, ya jawo fushi tsakanin matasa.

Shugaban kungiyar Benin Solidarity Movement (BSM), Elder Curtis Eghosa Ugbo, ya yi gargadin cewa ‘yan asalin Benin za su yi duk abin da za su yi don hana nada wani sarki a cikin garin, jaridar The Punch ta ruwaito.

Ya ce:

“Wannan ba zai taba faruwa a masarautar Benin ba, mu Benin ne.”

Wata kungiya, Great Benin Descendants (GBD), ta ce za ta toshe wurin da ake shirin nadin sarautar.

Babban jagoran kungiyar, Imasuen Izoduwa, ya bayyana taron a matsayin shirme. Ya ce garin Benin ba zai iya samun Oba da Sultan ba.

Wani shugaban matasa, Kwamared Amos Ehinomen Uagbor ya ce:

“Ana iya samun wannan a wani wuri? Shin ya kamata a yanzu mu samu OBA da Sultan a jahar Edo? A gaskiya, ya kamata a rufe wurin taron. ”

Batun ya kuma haifar da martani daga rukunin Facebook da aka sani da dandalin siyasar Edo.

Ya ce:

“Akwai tambayoyi da yawa game da wannan: Me ke faruwa a nan?

“Me zai sa Shuwa Arab su sami Sarki a masarautar Benin? Me yasa Enogie na Eyaen zai ba da damar wannan taron a yankinsa da otal ɗinsa?

“Za mu iya gwada wannan a Arewa? ”

Wani mamba na kungiyar, Goliath Marcus Garvey, ya yi zargin cewa wani shiri ne na kwace masarautar Benin.

Ya ce:

” Haka suka yi suka kama Illorin. Yanzu suna matsowa kusa.”

 

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here