Najeriya: Shugaban Kasar ya Kafa Kwamitin Sayar da Kadarorin da Aka Kwato Daga Hannun Mabarnata
Shugaban kasa Muhammadi Buhari ya amince da kafa kwamitin sayar da kadarorin gwamnati da aka kwato daga hannun mabarnata.
Ministan shari’a, Abubakar Malami, ya rantsar da kwamitin ranar Litinin a Abuja.
Shugaban kwamitin, Dayo Apata, ya bayar da tabbacin cewa kwamitin zai yi aiki da gaskiya, ba tare da boye komai ba, wajen sauke nauyin da aka dora masa Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin mutane 22 tare da bashi wa’adin wata shidda domin ya sayar da Kadarorin da aka kwato daga hannun mabarnata.
Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ne ya sanar da hakan yayin rantsar da kwamitin a ranar Litinin.
A cewar Malami, tun a ranar 27 ga watan Oktoba, 2020, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da mambobin kwamitin.
Malami ya bayyana cewa; “an zakulo mambobin kwamitin ne daga hukumomin gwamnati da ke da alaka da yaki da cin hanci, rashawa, da ta’annati.”
Read Also:
Ministan ya sanar da cewa Dayo Apata, babban mai nazarin shari’o’i a tarayya, shine zai jagoranci kwamitin.
A cewar Malami, daga cikin nauyin da aka dorawa kwamitin akwai gaggauta sayar da Kadarorin da aka kwato domin gwamnati ta samu kudaden shiga.
“Aikinku shine tabbatar da sayar da dukkan kadarorin gwamnati da aka kwato tare da sayar da su a cikin Najeriya domin gwamnati ta samu kudin shiga cikin gaggawa.
“A saboda haka, ina son wannan kwamiti ya yi aiki da hukumomin gwamnati masu alaka da aikinsu domin samun saukin gudanar da aiki kuma bisa tsarin doka.
“Ina fatan cewa wannan aiki da zaku yi zai zama sanadin samarwa gwamnati kudaden shiga da za a samu damar yi wa kasa aiki da su.
“Dole na gargadeku cewa ba karamin aiki bane a gabanku, akwai bukatar ku tsare kimar ku da ta kasarku. Akwai tsammani mai yawa a kanku,” a cewar Malami.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin, Apata, ya bayar da tabbacin cewa kwamitin zai yi aiki da gaskiya, ba tare da boye komai ba, wajen sauke nauyin da aka dora masa.