Namadi Sambo: Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa ya Kai wa Shugaba Buhari Ziyara

Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a Aso Rock da ke Abuja.

Shugabaan kasa Buhari da Namadi Sambo sun shiga ganawar sirri kuma a halin yanzu ba a tabbatar da dalilin ziyarar ba.

Sambo, tsohon gwamnan jihar Kaduna ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa ne a karkashin mulkin shugaba tsohon Goodluck Jonathan.

Shugaba Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Namadi Sambo, sun yi ganawar sirri a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata 22 ga watan Disamba.

Hadimin shugaban kasa a bangaren sabbin kafafen watsa labarai, Bashir Ahmad ya bayyana hakan ta shafinsa na Twitter @BashirAhmaad.

A halin yanzu dai ba a sanar da dalilin ganawarsu ba ko abinda suka tattauna. sambo dan jam’iyyar adawa ce Peoples Democratic Party ne yayin da shugaba Buhari dan APC ne.

Sambo shine mataimakin shugaban kasa a karkashin mulkin shugaban kasa Goodluck Jonathan. Kafin ya zama shugaban kasa shine gwamnan jihar Kaduna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here