NDLEA ta yi Nasarar Kama Wani Mai Fataucin Miyagun Kwayoyi

 

Da wuya mafarkin Adendu Kingsley mai shirin zama ango ya zama gaskiya bayan hukumar NDLEA ta kama shi.

Jami’an hukumar ne suka kama mai shirin zama angon dauke da haramtaccen sinadari.

Sai dai bai daura laifin abunda ya same shi a kan kowa ba, inda yace lallai yana sane da hatsarin da ke tattare da hakan a lokacin da zai yi tafiyar.

Hukumar hana sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi watau NDLEA, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja ta kama wani ango da ke shirin aurensa.

Lamarin ya shafi Elechi Adendu Kingsley, wani dan Najeriya mai shekaru 39 wanda aka kama da wata jakar leda a yayin tantancewa a jirgin Habasha mai lamba Et 911., PR News ta ruwaito.

Kinsley, dan asalin karamar hukumar Umulolo da ke jihar Imo wanda ke zama a Brazil tsawon fiye da shekaru 13 da suka gabata yace ba zai daura laifin kama shi da aka yi akan kowa ba.

“Ni ba yaro bane kuma na san abunda na sanya kaina a ciki. Na yarda cewa wani ne ya bani amma ni na bukaci cewa zan dauka.”

In ji shi. Kingsley ya ce an yi masa alkawarin naira miliyan 3 da zaran ya kai kwayoyin ga wani mutum a Najeriya lafiya.

Ya zo Najeriya ne domin shirye shiryen aurensa da za a yi a watan Janairun 2021.

Da yake magana a kan wannan sabbin dabaru na fataucin kwayoyi, Kabir Sani Tsakuwa, kwamandan NDLEA filin jirgin saman Abuja, yace tunanin masu fataucin miyagun kwayoyi ya zarta yadda ake zato.

“Abunda ake so damu shine kada mu tsaya a inda tunaninsu yake illa kawai mu dunga zartasu a tunani. Kamar yadda kuka gani, duk wani yunkuri da suka yi, muna sama da su, ga sakamakon hakan muna gani. Ina musu alkawarin sai na birkita tunaninsu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here