Neja Delta ta Kasance Tare da Jam’iyyar PDP tun Shekarar 1999 Zuwa yau Kuma 2023 ba Zata Zama Bare ba – Farah Dagogo

 

Ɗan majalisar wakilan tarayya na PDP daga jihar Ribas ya mara wa takarar Atiku Abubakar baya a zaben 2023.

Farah Dagogo ya bayyana shirinsa na haɗa kan mutum miliyan 10m a baki ɗaya Neja Delta don tabbatar da goyon bayan yankin ga Atiku.

A kwanakin baya jami’an tsaro sun damƙe ɗan majalisar bayan gwamna Nyesom Wike ya zarge shi da rura wutar matsalar yan asiri.

Rivers – Mamban majalisar wakilan tarayya, Farah Dagogo, ya ayyana cikakken goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, da abokin takararsa, gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.

Dagogo, mai wakiltar mazaɓar tarayya Degema/Bonny a jihar Ribas, ya ce nan ba da jimawa ba zai shirya tattakin mutane miliyan 10m a jihohin yankin Neja Delta domin Atiku/Okowa.

Channelst TV ta rahoto a wata sanarwa da hadimin ɗan majalisar, Ibrahim Lawal ya fitar, ya ce zai shirya Macin ne domin nuna wa duniya cewa har yanzu yankin na PDP ne.

Dalilin da yasa Neja Delta zata zaɓi PDP, Atiku – Dagogo

Farah Dagogo ya yi fatali da raɗe-raɗin cewa mutanen yankin Neja Delta zasu juya wa PDP baya sakamakon kayen da Gwamna Wike ya sha hannun Atiku a zaɓen fidda gwani da wasu dalilai.

Ɗan majalisar ya ce, “Neja Delta ta kasance tare da jam’iyyar PDP tun shekarar 1999 zuwa yau kuma 2023 ba zata zama bare ba.”

A cewarsa, mutanen yankin Neja Delta ba zasu mance da yadda jam’iyyar PDP ta yi sanadin samar da shugaban ƙasa daga yankin su watau Goodluck Jonathan.

“Kar ku yarda a yaudare ku, tsarin zaɓen Najeriya yanzun ya canza, karfin iko na hannun masu katin zaɓe. Ba wanda zai yanke wa mutane wanda zasu zaɓa ko waye shi sabida mutane ke da wuka da nama kan katin zaɓen su.”

Ɗan majalisar ya kara da cewa Atiku zai lashe zaɓe domin haka ne ribar waɗan da ba su son a barsu a baya ko a watsar da su a kwandon sharar jam’iyya.

Rikicin Dagogo da Wike

A watan Afrilu, Gwamna Wike ya ayyana nema da kame Dagogo duk inda aka ganshi bisa zargin ɗaukar nauyin ƴan asiri su tarwatsa taron tantance yan takarar PDP a Sakatariya da ke Patakwal.

Ɗan majalisar, wanda ke neman takarar gwamna karkashin inuwar PDP a wancan lokacin, ya shiga hannun jami’an tsaro bayan umarnin Wike.

Sai dai Babbar Kotu a Patakwal ta bayar da Belinsa kan miliyan N20m bayan shafe kusan wata ɗaya ana kai ruwa rana a shari’ar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here