Har Yanzu Ina Neman Wanda Zai yi Min Mataimaki – Tinubu

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu, ya ce har yanzu yana neman wanda zai yi masa mataimaki.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Abuja, a lokacin kaddamar da wani littafi a bikin cika shekara 60 da haihuwar Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila.

Dan takarar yana da dama har zuwa ranar 15 ga watan Yuli kamar yadda hukumar zaben kasar ta tanada ya mika mata sunan wanda zai maye gurbin Kabir Ibrahim Masari, wanda ya bayar da sunansa domin rike wannan mukami na wucin-gadi.

Tinubu, ya yaba wa Kakakin Majalisar Wakilan a kan irin gudummawar da ya ce yana bayarwa ga dumokuradiyya, yana mai cewa abin da ya yi masa a lokacin zaben fitar da gwani abu ne da ba zai iya ambatawa ba a wannan lokaci.

Ya ce, ”Na kashe lokaci mai yawa, lokaci da dama, mutane za su iya kagara, za su iya kyashi, za su iya bakin-ciki ma. Na yi gagarumar nasara, na gode ma.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here