Yadda Shahararren Dan Wasan Kwallon Kafa yake Cin Duniyarsa da Tsinke – Neymar

Kasaitaccen dan wasan kwallon kafan nan dan asalin Brazil, Neymar, yana cin duniyarsa da tsinke.

Idan mutum ya kalli gidan da yake zama, na kimanin N3,300,000,000, zai yarda cewa wata miyar sai a makwabta.

Batun motar da yake murzawa ta kece raini kirar Ferrari, mai kimanin tsadar N130,000,000, sai dai a ce aljannar duniya.

Neymar yana rayuwa cikin wani katafaren bene mai hawa 5 a Paris, wanda aka kimanta tsadar shi zai kai N3,300,000,000, kuma yana hawa motarsa kirar Ferrari mai kimar N130,000,000.

Matashin mai shekaru 28 da haihuwa ya koma hadadden gidan nasa a 2017, inda ya cigaba da cin duniyarsa da tsinke.

An gina katafaren gidan ne tun 1950 amma asali gidan wani jarumin Faransa ne mai suna Gerard Depardieu. Ginin yana da tsawon kafa 10,800, kuma yana da wurin wanka mai kayatarwa.

Hamshakin dan wasan kwallon kafar yana da wani bangare na wasanni, da kuma dakin wanka mai buregewa.

Duk bakon da zai kai masa ziyara ba zai so ya bar wurin ba, saboda morewa, don gidan aljannar duniya ne a Paris.

Duk da dai SunSport ta ruwaito cewa gidan ba nashi bane, yana hayar gidan ne, kuma duk wata yana biyan N5,000,000.

Yana samun a kalla £550,000 duk mako, kuma hakan ba komai bane idan aka hada shi da albashinsa na kowanne wata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here