Ni Mai Gaskiya ne Kuma Gaskiya Zata Wanke Ni – Abba Kyari

 

Bayan dakatad da shi, Abba Kyari ya aike sakon godiya ga mutanensa.

Ya jaddada cewa shi mai gaskiya ne kuma gaskiya zata wanke shi.

Hukumar yan sanda ta kaddamar da bincike kan sa.

Hazikin dan Sanda, DCP Abba Kyari, wanda aka dakatar ya jaddada cewa shi fa yana da gaskiya kan tuhumar da ake masa kuma nan ba da dadewa ba gaskiya zai bayyana.

Abba Kyari ya sake magana ne a jawabin da ya daura a shafin yanar gizon tsaffin wadanda suka halarci wani taro a Amurka, ThisDay ta gano.

Yace dukkan abubuwan da ya fada kuma ya daura a shafinsa gaskiya ne.

Wani sashen jawabin yace:

“Ga dukkan abokai ne da abokan aiki na a ofis, kada ku damu. Ina cikin koshin lafiya da ba na cikin damuwa.”

“Dukkan wadanda suka san ni sosai sun san ba na son karya. Dukkan abinda na fada ko na wallafa gaskiya ne. Nan ba da dadewa ba gaskiyar lamarin nan zata bayyana.”

“Mun godewa Allah bamuyi rashin wani sashen jikinmu a dukkan hare-hare masu haduran da kuma kai ba a fadin tarayya.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here