Nimet ta yi Gargaɗi Kan ɓullar Cutar Sanƙarau
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya Nimet ta yi gargaɗin cewa wasu jihohin arewacin ƙasar na ƙara fuskantar barazanar ɓarkewar cutar sanƙarau.
Nimet a cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, ta ce jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara da Katsina da Kano da Jigawa da Bauchi da Yobe da Gombe da kuma Borno su ne suka fi fuskantar barazanar.
Read Also:
Hukumar ta kuma ce alamomin cutar sanƙarau sun haɗa da zazzaɓi mai zafi da ciwon kai mai tsanani da riƙewar wuya da amai, sai rashin son kallon haske da ruɗewa da kuma ƙuraje.
Nimet ta kuma ƙara da cewa ana iya kamuwa da cutar da hanyar mu’amula da masu ɗauke da cutar da kuma shiga cunkoso, inda ta buƙaci alumma su yi rigakafi su wanke hannu su kuma gujewa kusantar masu cutar su kuma rufe bakinsu da hanci.
Hukumar ta kuma yi kira ga alumma da su yi gaggawan zuwa asibiti idan sun ji alamomin da aka bayyana.