Kano: NNPP ta yi Martani Kan Cewa ƴan Jam’iyyar na Sauya sheka

 

Jihar Kano – Jami’yyar NNPP ta yi zazzafan martani kan cewa ƴaƴanta suna sauya sheka zuwa APC.

Shugaban NNPP, Hashimu Dungurawa ya ce sam ba gaskiya cikin lamarin domin kansu a hade yake a jihar Kano.

Legit ta samo martanin da NNPP ta yi ne a cikin wani sako da daraktan yada labaran Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.

NNPP ta ce ƴaƴanta ba sa sauya sheka

Jami’yyar NNPP a jihar Kano ta fitar da matsaya kan ƴaƴanta da ake cewa suna sauya sheka a Abuja zuwa APC.

Shugaban NNPP, Hashimu Dungurawa ya ce sam ba gaskiya cikin labarin domin har yanzu ba su ga ko mutum daya ya ragu a cikinsu ba.

Ga abin da yake cewa:

Mun ji labari wani mutum a Abuja (Sanata Barau Jibrin) yana karbar yan NNPP zuwa APC amma wannan labarin ba gaskiya ba ne.

Mun duba rajistar mambobin mu amma har yanzu ba muga ko daya ya ragu ba.

– Hashimu Dungurawa, Shugaban NNPP a Kano.

NNPP ta ba Sanata Barau shawara

Shugaban NNPP, Hashimu Dungurawa ya ce ya kamata idon Sanata Barau Jibrin ya bude a kan mutanen da yake karba a Abuja.

Hashimu Dungurawa ya ce ya kamata Sanata Barau ya yi hankali da yan damfara masu zuwa suna karbar kudi a wajensa da sunan sauya sheka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here