ALLAH ya yi wa Mataimakin Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Mai Ritaya, Nuhu Aliyu Rasuwa
Gwamnatin jahar Neja ta bayyana kaduwa kan rasuwar mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya mai ritaya, Nuhu Aliyu.
Ana yiwa Aliyu wanda ya wakilci yankin Neja ta Arewa a majalisar dattawa kallon dattijo mai daraja.
Marigayin sanatan yana daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar Peoples Democratic Party a jahar Neja.
Jahar Neja – Nuhu Aliyu, tsohon sanata wanda ya wakilci yankin Neja ta Arewa a majalisar dattawa, ya rasu.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Aliyu wanda ya kasance mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda mai ritaya ya rasu a ranar Laraba, 4 ga watan Agusta, bayan gajeriyar rashin lafiya.
Ya rasu yana da shekaru 79 a duniya.
Gwamnatin jahar Neja ta tabbatar da mutuwar tsohon dan majalisar.
Read Also:
Sakataren gwamnatin jahar Neja, Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana rasuwar Aliyu a matsayin babban rashi.
Matane ya ce: ”Kishin kasa da kyakkyawar riko wajen gudanar da ayyukan majalisa game da jin dadin jama’a da marigayi Sanata Nuhu Aliyu ya nuna sun cancanci ayi koyi da su.
“Amma dole ne mu yarda da cewa daga Allah muke kuma gare Shi duk za mu koma. Babu wanda zai rayu fiye da lokacin da Allah Madaukakin Sarki ya diban masa.”
Wata majiya daga ahlinsa ta shaida wa jaridar This Day cewa za a yi jana’izar dan sandan mai ritaya a makabartar Barnawa da ke Kaduna da misalin karfe biyu na ranar Laraba, 4 ga watan Agusta, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Marigayi dan siyasar ya kasance jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party na farko a jahar Neja kafin a zabe shi a majalisar dattijai a 1999 sannan aka sake zabar shi kan wannan matsayi a 2003 da 2007.