Peter Obi ya Hakura ya Barwa Kwankwaso Matsayin Shugaban Kasa –  NNPP

Wani sabon al’amari ya kunno kai yayin da ake ci gaba da kokarin ganin an yi maja tsakanin jam’iyyar NNPP da Labour Party.

A yanzu haka, NNPP ta ce hanya guda da za a iya samun maslaha tsakanin jam’iyyun biyu shine Peter Obi ya hakura ya barwa Kwankwaso matsayin shugaban kasa.

Tun farko dai tsohon gwamnan na jihar Kano ya tabbatar da cewa ana kan tattaunawa tsakaninsu da jam’iyyar Obi.

Abuja – Kakakin kungiyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Mista Major Agni, ya bayyana cewa sharadi guda na yin maja tsakaninsu da Labour Party (LP) shine cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi ya yarda ya zama abokin takarar Rabiu Musa Kwankwaso.

Da yake jawabi a talbijin din Arise a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, kakakin na NNPP ya bayyana cewa Kwankwaso ne ya yi nasara cikin yan takarar shugaban kasa 18 a zaben da suka yi kuma har yanzu shine suka fi so ya zama shugaban kasar Najeriya.

Ya dage cewa jam’iyyar na ci gaba da samun kiraye-kiraye cewa lallai kada Kwankwaso ya janyewa Obi, yana mai cewa maslaha daya shine Obi ya yarda ya zama mataimakin Kwankwaso.

Ya bayyana cewa Kwankwaso ya sauya rayukan talakawa, yana mai cewa akwai bukatar a barshi ya jagoranci yarjejeniyar LP/NNPP, jaridar Thisday ta rahoto.

Ya ce:

“Muna ci gaba da samun kiraye-kiraye. Mutane da dama sun kira suna fadin cewa, a’a, ba za mu yarda da wannan ba. Wannan shine kawai abun da muke so ku cimma matsaya a kai cewa Peter ne zai zama mataimaki.”

Agbo ya jadadda cewa koda dai Obi mutumin kirki ne wanda shima ya yi namijin kokari, ba zai yiwu ace ya yi jagoranci ba a duk yarjejeniyar da za a cimma game da zaben shugaban kasar 2023.

Ya kuma karyata cewa Kwankwaso na da karfi ne a iya Kano da Jigawa, yana mai cewa duk wanda ya yarda da hakan toh an batar da shi ne, ya kuma ce jam’iyyar ta shafe tsawon shekaru 21.

Ya kuma yi watsi da rade-radin cewa jam’iyyar NNPP/LP ta shirya kawance ne kawai don ruguza jam’iyya All Progressives Congress (APC) mai mulki da jam’iyyar adawa ta PDP, yana mai cewa jam’iyyun a shirye suke su karbi mulki.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here