Gwamna Ododo ya Ƙarawa Ƴan Fansho Kudin Alawus Duk Wata

Jihar Kogi – Gwamnan Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya amince da biyan N10,000 a matsayin alawus ga dukkan ƴan fansho a jihar.

Ahmed Ododo ya ɗauki wannan mataki ne bayan karɓar rahoto daga shugaban ma’aikatan jihar Kogi, Mr Elijah Evenemi a fadar gwamnatinsa da ke Lokoja.

Ya jadada kudirin gwamnatinsa na fifita walwalar al’umma, inda ya yabawa ƴan fansho bisa shafe shekaru suna yiwa jihar Ƙogi hidima, rahoton Leadership.

Gwamna Ododo ya ɗaukarwa ƴan fansho alƙawari

Gwamnan ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ɗora ne daga wurin da uban gidansa, tsohon gwamna Yahaya Bello ya tsaya.

Ya ƙara da cewa duk ɗan fanshon da ke karɓar ƙasa da N50,000 a wata za a sa shi a tsarin knshorar lafiya a matakin jiha da kananan hukumomi, cewar Daily Post.

Gwamna Ododo ya bayyana cewa tun da ya hau kan madafun iko, ƴan fansho ba su sake samun tangarɗa wajen biyansu haƙƙokinsu ba a kowane ƙarshen wata.

Ƴan fansho sun yabawa gwamnan Kogi

Tun da farko, shugaban kungiyar ’yan fansho ta jihar, Mista Ohida Otaru ya yaba wa gwamnan bisa yadda ya ɗauki tsofaffin ma’aikata da muhimmanci.

Mista Otaru ya ce shekaru 20 kenan ba a waiwayi halin da ƴan fansho ke ciki ba sai da Gwamna Ahmed Ododo ya zo.

Ya yabawa gwamnan musamman kan yadda ya ƙara kudin fansho da ake ba ma’aikatan da suka yi ritaya, wanda ya ce zai taimaka matuka wajen inganta rayuwarsu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here