Ofishin Hukumar Zaɓe ta ƙasa a Jahar Akwa Ibom ya Kama da Wuta
An cinna wa Wani ofishin hukumar zaɓe ta ƙasa wuta a jahar Akwa Ibom, Kwamishinan hukumar INEC na jahar ya tabbatar da faruwar lamarin.
Wannan na ƙunshe ne a wani sako da INEC ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta Tuwita.
Hukumar tace irin waɗannan hare-haren ka iya maidawa INEC hannun agogo baya yayin da take gudanar da shirye-shiren babban zaɓe mai zuwa a shekarar 2023.
Wani Ofishin ƙaramar hukuma na hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) a jahar Akwa Ibom ya kama da wuta.
Kwamishinan zaɓen jahar, Barr. Mike Igini, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Legit.ng ta ruwaito cewa, INEC ta bayyana haka a wani sako da ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta Tuwita.
Hukumar zaɓen tace Wutar ta kama ne da sanyin safiyar yau Lahadi, 2 ga watan Mayu, 2021 a ofishinta dake ƙaramar hukumar Essien Udim, jahar ta Akwa Ibom
Read Also:
Jawabin da hukumar tayi ya nuna cewa wutar tayi ɓanna a ofishin inda ta lalata Akwatunan zaɓe guda 345, da kuma teburan jefa kuri’a 135, wayoyin hannu, tankin ruwa da kuma kayayyakin cikin ofis ɗin.
Rundunar yan sanda, waɗanda suma suke fama da irin wannan harin, sun san da faruwar lamarin kuma sun fara bincike a kan lamarin.
INEC tace:
“Waɗannan hare-haren da ake kaiwa kwanan nan akan kayayyakinmu bayan mun kammala kai kayayyakin zaɓe a faɗin ƙasar nan saboda ƙaratowar zaɓen 2023 abun damuwa ne matuƙa.”
“Idan ba’a cigaba da kulawa yadda yakamata ba, Waɗannan hare-haren zasu iya maida mana hannun agogo baya a kan dukkan ayyuakan da hukumar tasa a gaba, waɗanda suka haɗa da; cigaba da gunanar da rijistar cancantar jefa ƙuri’a da sauran su.”
“Amma duk da haka, hukumar na tabbatarwa yan Najeriya cewa zata maida komai yadda yake kafin faruwar lamarin a Akwa Ibom., kuma zata cigaba da shirye-shiryen zaɓe yadda yakamata.”