ƙungiyar Ohanaeze ta ƙabilar Ibo ta yi Kira ga Gwamnatin Najeriya ta Tabbatar an Kai Kanu kotu

 

Gabanin gurfanar da Nnamdi Kanu, shugaban ƴan awaren Biafra na IPOB a gaban kotu ranar Alhamis, ƙungiyar Ohanaeze ta ƙabilar Ibo ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tabbatar an kai Kanu kotu.

Jaridar Vanguard a Najeriya ta rawaito cewa ƙungiyar ta Ohanaeze ta ce bayyanar Kanu a kotu na da muhimmanci don nuna wa duniya cewa Nnamdi Kanu na ciki ƙoshin lafiya kuma za a yi masa adalci a lokacin shari’a.

Idan ba a manta ba, ƙungiyar IPOB ta yi barzanar rufe duka ayyuka a Kudu masu gabashin ƙasar idan ba a kai shugaban nasu gaban kotu ba aranar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here