Matamakin Shugaban Kasan Najeriya, Yemi Osinbajo ya Yabi Aisha Buhari

Farfesa Yemi Osinbajo ya yabi Mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari.

Yemi Osinbajo ya ce ba a taba ganin uwargidar shugaban kasa irinta ba.

Mataimakin shugaban kasar ya ce za ba za a manta da Aisha Buhari ba Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana Hajiya Aisha Buhari da matar da ta canza salon ofishin uwargidar shugaban kasa.

Jaridar The Nation ta rahoto Farfesa Yemi Osinbajo ya na cewa Aisha Muhammadu Buhari mata ce wanda ta sha dabam da duk sauran takwarorinta.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Yemi Osinbajo ya ce Aisha Buhari ta sha banbam da sauran matan shugabannin kasan da aka yi a tarihin Najeriya.

A cewar Osinbajo, dabi’ar Hajiya Aisha Buhari ne ya jawo mata farin-jini wajen al’ummar Najeriya.

Osinbajo ya ce daga cikin inda Aisha Buhari ta banbamta da sauran matan shugabannin da aka yi a baya shi ne ta bude shafukan sada zumunta a kafafen zamani.

“Da wahala a ce an yi wata uwargidar shugaban Najeriya a baya wanda a cikin kankanin lokaci ta shiga zuciyar mutane sosai kamar Aisha Buhari.” Inji Osinbajo.

“Ita ce uwargidar shugaban Najeriyar farko da aka gani a shafin Twitter, Instagram da sauran dandalin sada zumunta na zamani, kuma aka san da zamanta.”

Osinbajo yake cewa: “Kuma watakila ita ce ta farko da ta ke samun ra’ayoyin ‘Yan Najeriya kai-tsaye.”

“Da ra’ayoyinta na kai-tsaye da fadan gaskiya da wasu ke ganin sun sha banbam wasu lokutan, ta jawo abin magana wajen ‘Yan Najeriya da har yau ba a daina ba.”

Mataimakin shugaban kasar ya ce Uwargidar mai gidansa ta fita dabam a dalilin taimakon jama’a da ta ke yi, ya ce za a dade ba a manta da ita a tarihin kasar nan ba.

Mai girma mataimakin shugaban Najeriyar ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin kaddamar da littafin da aka rubuta a game da mai dakin shugaban kasa dazu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here