Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo zai Zama Shugaban Kasan Najeriya – Fasto gaisiehas

Wani Shugaban addini a kasar Ghana, Prophet Nigel Gaisiehas ya yi wasu hasashe game da abubuwan da yake ganin za su faru a nan gaba.

Daya daga cikin hasashen ya kasance game da makomar siyasar mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Osinbajo bai saki kowani jawabi game da shirinsa bayan barin kujerarsa a 2023.

Wani fasto mazaunin kasar Ghana, Prophet Nigel Gaisie, ya yi hasashen cewa mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo zai zama Shugaban kasar Najeriya.

BBC ta ruwaito cewa faston, wanda ya kasance Shugaban cocin Prophetic Hill Chapel Prophet ya yi hasashen a lokacin wa’azinsa na shiga 2021.

Ya ce:

“Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo zai zama shugaban kasa.”

Sai dai Gaisie, bai yi bayani kai tsaye ba kan ko hasashensa kan Osinbajo zai zo ne bayan gwamnatin Buhari ko kuma wani lokaci a nan gaba.

Faston ya kuma ce koda dai duniya za ta samu zaman lafiya, za a aiwatar da wani harin ta’addanci a kasar Amurka. Ya kuma yi hasashen cewa wani shahararren mai wa’azi zai mutu a 2021.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here