Gwamnatin Osun ta Sanya Dokar Hana Fita a ƙananan hukumomi 2 na Jihar

 

Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya sake sanya dokar hana fita a wasu ƙananan hukumomi guda biyu na jihar.

Aɗeleke ya sanya dokar hana fitan ne biyo bayan rikicin filaye da ya sake ɓarkewa a tsakanin al’ummomin ƙauyukan Ilobu da Ifon.

Sanarwar sanya dokar hana fitan wacce ta fito ta hannun kwamishinan watsa labarai na jihar, ta ce dokar ta koma daga ƙarfe 6:00 na dare zuwa ƙarfe 6:00 na safe.

Jihar Osun – Gwamnatin jihar Osun ta sanya sabuwar dokar hana fita a ƙananan hukumomin Irepodun da Orolu na jihar, biyo bayan rikicin ƙabilanci tsakanin al’ummar ƙauyukan Ilobu da Ifon.

Idan dai za a iya tunawa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sanya dokar hana fita a ƙananan hukumomin biyu a farkon watan Satumba, bayan da aka samu rikici tsakanin ƙauyukan biyu.

Daga baya an sassauta dokar hana fita bayan hankula sun kwanta a yankin, rahoton Tribune ya tabbatar.

Meyasa aka sake sanya dokar?

Sai dai, wata sanarwa da Kolapo Alimi, kwamishinan watsa labarai da wayar da kan jama’a na jihar, ya fitar a ranar Laraba, ta ce Adeleke ya bayar da umarnin a mayar da dokar hana fita a ƙananan hukumomin biyu, biyo bayan rikicin da ya ƙara ɓarkewa a ƙauyukan.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

“Biyo bayan sake ɓarƙewar rikicin ƙabilanci tsakanin mutanen ƙauyukan Ilobu da Ifon, gwamnatin jihar Osun ta ba da umarnin dokar hana fita ta cigaba da aiki a ƙauyukan da lamarin ya shafa.”

“Lokacin dokar hana fitan ya koma ƙarfe 6:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe. Za a taƙaita zirga-zirgar mutane da ababen hawa yayin dokar har sai an samu sabuwar sanarwa.”

“Hakan wajibi ne domin daƙile yunƙurin lalata rayuka da dukiyoyi a cikin wannan lokacin, saboda rikicin filaye.”

“Duk wanda aka kama yana yawo a ƙananan hukumomin Irepodun da Orolu a lokacin dokar hana fitan, za a cafke shi tare da fuskantar hukunci.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com