Bayan Taron Gaggawa: Jam’iyyar PDP ta Yanke Shawarwari Akan Hada Kan Mambobinta

Jam’iyyar Peoples Democratic Party ta fara shirin hada kan dukkan fusatattun mambobinta.

Kola Ologbodiyan, sakataren jam’iyyar PDP na kasa, ya sanar da hakan a wani bidiyo na Facebook a ranar Talata, 3 ga watan Agusta.

Ologbodiyan ya ce kafa tsarin warware rikicin wani bangare ne na shawarar da jam’iyyar ta yanke a wani taro a ranar Talata.

A kokarinta na kawo karshen rikicin da ke barazana gare ta, jam’iyyar PDP a yayin taron ta na gaggawa a Abuja a ranar Talata, 3 ga watan Agusta, ta yanke wasu muhimman shawarwari.

A cikin wani bidiyon Facebook na PDP, kakakin jam’iyyar adawa ta kasa, Kola Ologbondiyan, ya sanar da wasu shawarwari da aka yanke cikin gaggawa.

Ologbodiyan ya bayyana cewa PDP za ta duba korafe -korafen da mambobin Kwamitin Aiki na Kasa (NWC) da na Majalisar Zartarwar jam’iyyar ta Kasa (NEC) suka gabatar.

Ya kuma bayyana cewa an hanzarta yin amfani da wata hanyar warware rikicin cikin gida don magance matsalolin da ke kasa.

Kakakin jam’iyyar ya ce PDP na kira ga duk masu ruwa da tsaki da membobin da abin ya shafa da su kwantar da hankulansu yayin da suke magance matsalolin baki daya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here