Fusatattun Mambobin PDP a Boron Sun Hana Dakataccen Shugaban Jam’iyyar Shiga Ofishinsa
Daruruwan fusatattun matasan PDP sun fatattaki dakataccen shugaban jam’iyyar a jihar Borno, Hon Zanna Gadama a ranar Lahadi, 3 ga watan Yuli.
Matasan sun hana Gadama shiga sakatariyar jam’iyyar da ke Maiduguri bayan ya kira wani taro na masu ruwa da tsaki da manema labarai.
Suna dai zargin dakataccen shugaban da wawure kudaden jam’iyyar da kuma yi mata zagon kasa don kada ta kai labari a zabe.
Borno – Fusatattun mambobin PDP a ranar Lahadi, sun mamaye sakatariyar jam’iyyar da ke Maiduguri don hana dakataccen shugaban jam’iyyar reshen jihar Borno, Alhaji Zanna Gadama, shiga ofishinsa don gudanar da wani taro da jawabi ga manema labarai.
Read Also:
Gadama ya gayyaci manema labarai don su nadi taron masu ruwa da tsaki da ya kira bayan dakatar da shi da wasu jami’an jam’iyyar suka yi kwanaki da suka wuce, Vanguard ta rahoto.
Sai dai kuma, da shigarsa sakatariyar ya tarar da magoya bayan jam’iyyar wadanda suka mamaye dakin taron inda suka bukaci ya fice daga harabar wajen.
Magoya bayan jam’iyyar wadanda suka yi tofin Allah tsine ga dakataccen shugaban sun zarge shi da wawure kudaden jam’iyyar tsakanin 2019 zuwa yau, jaridar Leadership ta rahoto.
Sun kuma sha alwashin cewa idan ba a tsige shi a matsayin shugaban jam’iyyar PDP a Borno ba daga jam’iyyar har dan takararta shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ba za su samu kuri’unsu ba.
Hakazalika, sun zargi shugaban jam’iyyar da hada kai da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar don kifar da jam’iyyar a duk shekarun zabe.