Jam’iyyar PDP ta Kara Rasa Mambobinta a Jahar Zamfara

Dubun dubatar mambobin jam’iyyar PDP sun yi kaura zuwa jam’iyyar APC a garin Kauran Namoda, jihar Zamfara.

Masu sauya shekar sun bayyana cewa sun bar PDP ne saboda rashin shugabanci a jam’iyyar.

Sauyin shekar mambobin jam’iyyar na zuwa a daidai lokacin da gwamna Nyesom Wike ke cewa ‘yan Nigeria sun kagu PDP ta karbi mulkin kasa a 2023.

Dubban ya’yan jam’iyyar PDP a mazaɓar Kungurki cikin ƙaramar hukumar Kauran Namoda suka canza sheka zuwa jam’iyyar APC, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Gungun mutanen, sun bayyana yin hijirar tasu ne a wani bikin karɓar su da aka shirya a Sabon Garin Kauran Namoda.

Da ya ke magana a madadin sauran mabiya, Malam Bala Kaura, ya ce kungiyoyi uku ne suka yanke shawarar barin jam’iyyar PDP su ka tsallaka APC sakamakon rashin shuagabancin da babu a jam’iyyar ta PDP.

“Babu wata nasara da za ka nuna sama da shekara guda da PDP ta kama mulki a wannan jihar” in ji malam Bala.

Da take tofa albarkacin bakinta, tsohuwar shugabar matan jam’iyyar PDPn, Malama Bilkisu, ta ce sun bar jam’iyyar ne saboda halin ko-in kula na jam’iyyar.

Ta ce tun hawan “Gwamnatin PDP ta manta da mu ba ma ganin wata nasara da ake cimmawa.

“Babu wani nasara da za ka nuna sama da shekara guda da PDP ta kama mulki a wannan jihar.
“A dan haka, amadadin ɗaukacin matan jam’iyyar PDP na mazaɓar Kungurki, ina mai sanar da ficewarmu daga PDP zuwa APC” in ji malama Bilkisu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here