PDP Zuwa APC: Kungiyar MURIC ta yi Magana Kan Sauya Shekar Femi Fani-Kayode

 

Kungiyar Kare Hakkokin Musulmai (MURIC) ta bayyana cewa sauya shekar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, kyakkyawan ci gaba ne.

Farfesa Ishaq Akintola, darakta kuma wanda ya kafa MURIC, ya bayyana wannan a cikin wata sanarwa da shi da kansa ya sa hannu.

A cewarsa, ya kamata a ga canjin zuciyar FFK daga kusurwa mai kyau, musamman ga waɗanda ke son ci gaban Najeriya a zuciya.

Lagos – Wata kungiyar kare hakkin Musulunci (MURIC), ta mayar da martani kan sauya shekar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode zuwa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kungiyar ta ce yan Najeriya za su samu riba sosai sakamakon ficewar Fani-Kayode zuwa APC.

Legit.ng ta tattaro cewa darakta kuma wanda ya kafa MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce “duk da guguwar sukar da ta gaishe da matakin FFK”, ficewarsa zai haifar da hadin kai a kasar.

PM News ta kuma ba da rahoton cewa MURIC, ta ce ba za ta shiga cikin waɗanda suka kalli batun ta kusurwa ɗaya kawai ba, ta kara da cewa za ta yi zurfin tunani mai nisa don ba ta damar ganin dukiya mai daraja da aka ɓoye a bayan manyan duwatsu.

Sanarwar ta ce:

“Fani-Kayode mutum ne wanda ya nuna rashin goyon baya ga masu neman ballewa, masu son kawo rauwa da masu neman ballewa. Najeriya ta karkata zuwa tafarkin yaki da rugujewa sakamakon tashin hankalin kungiyoyin da yake marawa baya, a yau, FFK a sabon sansaninsa yana iya inganta hadin kan Najeriya.

“Dansa, Cif Femi Fani Kayode, a yau ya sake yin irin wannan musabaha a fadin Nija. Yakamata a duba canjin zuciyar FFK daga kusurwa mai kyau, musamman ga waɗanda ke nufin Najeriya da alheri.”

MURIC ta kuma yabawa Buhari saboda hakurin da ya yi da masu sukarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here