Gwamna Yahaya Bello ya Bayyana Cewa Akwai Gwamnonin PDP da ke Shirin Komawa APC

 

Gwamna Yahaya Bello na jahar Kogi yace wasu gwamnonin PDP na shirin komawa APC.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a Abuja bayan taron sirri da suka yi da ‘yan kwamitinsa.

Bello ya sanar da hakan ne yayin da ake rade-radin cewa Gwamna Matawalle zai sauya sheka Gwamnan jahar Kogi kuma shugaban kwamitin tuntuba na jam’iyya mai mulki ta APC, Yahaya Bello, ya ce gwamnoni masu yawa daga jam’iyyar PDP da sauran manyan jam’iyyu na kokarin komawa APC.

Wannan na zuwa ne bayan rade-radin da ake yi na cewa gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle, ya shirya tsaf domin barin jam’iyyar PDP zuwa APC.

“Ina da kwamitin matasa, mata da kuma masu nakasa wanda muke janyowa jam’iyyarmu.

“Kamar yadda muke janyo matasa, mata da masu nakasa, haka muke kokarin janyo ‘yan wasu jam’iyyun siyasa da suka hada da gwamnoni.

“Idan zaku tuna, akwai matasa da kuma matasa a zukatansu. Hakan yasa muke kokarin kawo su cikin jam’iyyarmu. Za ku gansu da yawansu.

“Na fadi muku, akwai wani gwamna daya da zai dawo jam’iyyarmu daga karshe kuma hakan zai sa sauran su garzayo saboda nan ne komai ke faruwa na cigaban kasar nan. “Hakan ne yasa nace muna kara karfi kuma muna samun cigaba a dunkule,” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here